
A yi gwaji don gano ko coronavirus ce ke hallaka mutane a Kano – Farfesa Usman Yusuf
Tuesday, 21 April 2020
Comment
Farfesa Usman Yusuf tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya kuma kwararren likita kan abin da ya shafi jini da bargon dan adam ya ce idan "har ba a kai wa jihar Kano dauki ba a wannan lokaci to jihar ka iya zama cibiyar cutar korona ta nahiyar Afrika".
Kano ka iya zama cibiyar korona a Afrika
Da ma dai hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi gargadin cewa Afrika za ta zama wurin da annobar korona za ta kyankyashe, kasancewar kasashen nahiyar na da karancin asibitoci da kuma halayyar shugabanninta na rashawa da cin hanci.
WHO ta ce "akwai fargabar mutum 300,000 ka iya mutuwa sannan kuma annobar za ta jefa kimanin mutum miliyan 30 cikin kangin talauci."
Daya daga cikin dalilan da hukumar ta bayar shi ne cunkoso a birane, wani abu da cutar take so domin yaduwa.
A 'yan kwanakin nan dai ana ta samun yawan mace-macen mutane musamman dattijai a birnin na Kano, inda makabartu ke samun ninkin gawarwakin da ake kaiwa a baya.
Hakan ne ya sa Farfesa Yusuf Usman alakanta mace-macen na Kano da annobar korona, inda ya ce ya kamata a bincika watakila korona ce ke kashe mutane a Kano.
A wani rubutu da kwararren likitan wanda ya kwashe shekaru 38 yana aiki a Amurka da Burtaniya da ma Najeriya ya yi, ya ce "rashin gwaji ne ya sa ba a iya tantance yawan masu dauke da cutar ba a Kano da ma arewacin kasar.
"Idan har za a samar da wuraren gwaji to watakila alkaluman da za a samu ka iya fin na jihar Legas yawa".
Ya kara cewa ''Mun san cewa wannan ciwo na Covid-19 ya fi yi wa dattijai illa. Kuma mun san cewa Kano tana da cunkoso kasancewar ta fi kowacce jiha yawan jama'a a fadin Najeriya."
Dangane da halayyar jama'a, Farfesa Usman ya ce "halayyar mutanen Kano ta rashin bin umarnin hukuma wajen zama a gida na taimaka wa cutar nan ci gaba da bazuwa".
''Har yanzu a Kano ana yin kwallon kafa. Ana taron biki da tarayya a masallatai ."
Da yake musanta batun cewa jama'a na mutuwa a Kano ne saboda yunwa sakamakon dokar kulle da gwamnatin jihar ta sanya, Farfesa Usman ya ce "me ya sa mutane ba sa mutuwa a Daura ko Kaduna ko Legas ko Fatakwal? Me ya sa sai a Kano?
''Cutar korona ce take fyadar 'ya'yan kadanya a jihar. Kuma dole ne a dauki mataki kafin al'amarin ya ta'azzara zuwa wasu jihohin masu makwabtaka a arewacin kasar kasancewar Kano ce mahada."
Mece ce mafita?
Farfesa Yusuf Usman ya zayyana wasu hanyoyi guda hudu da ya ce su ne kawai mafita:
Gwamnatin tarayya ta kai dauki Kano
Hana mutane cudanya
Bincike da yin gwajin cutar
Kayan aiki ga likitoci da sauran ma'aikata
Gwamnatin Tarayya ta kai dauki Kano:
Farfesa Usman ya ce wannan annoba bisa la'akari da girmanta ta fi karfin Kano saboda haka dole ne sai gwamnatin tarayya ta kai wa Kano dauki ta hanyar samar da kayan aiki da kuma tallafin abinci ga mutanen.
Hana mutane zirga-zirga:
Kwararren likitan yana da ra'ayin cewa idan dai har gwamnati na son shawo kan wannan annoba a jihar ta Kano, to dole ne sai ta hana mutane cudanya da juna ta hanyar sanya dokar zama a gida. To amma kuma ya ce " ba zai yiwu ba a kulle mutane musamman irin al'ummar Kano a cikin gidaje ba tare da an sama musu abinci ba. Saboda haka a nan ne ya kamata gwamnatin tarayya ta shigo ciki."
Bincike da yin gwaji:
Farfesa Usman ya ce dole ne a bude cibiyoyin gwaji domin gano masu dauke da cutar. Har wa yau, sai an dauki ragamar yin bincike a cikin al'umma domin zakulo da killace duk wanda aka samu na dauke da cutar.
Kayan aiki ga likitoci da sauran ma'aikatan asibiti:
A nan farfesa ya musanta irin zargin da ake yi wa likitoci na kin karbar marasa lafiya da ke zuwa asibiti, inda ya ce akwai fargaba a tsakanin likitoci tun da ba su da kayan aiki irin wadanda hukumar lafiya ta duniya ta amince da su kamar kayan kariya da takunkumin fuska da gilashi da safar hannu da takalmin kariya da dai sauransu.
Ya ce "shi likita tamkar soja yake a filin yaki. Idan ka kai soja filin yaki babu makami babu abin da zai iya yi. To haka likita yake a asibiti."
Idan annoba ta samu Kano tamkar ta kama Arewa ne
Kasancewar birnin Kano cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya da kuma yawan jama'ar da ke cikinsa ya sa mutane da dama da suka hada da masana fargabar yanayin da yankin arewa zai kasance a duk lokacin da wata annoba ta afka wa birnin.
Kusan za a iya cewa idan ban da wasu daga cikin jihohin arewa ta tsakiya, dukkan ragowar jihohin arewa maso yamma da gabas na shige da fice a Kano domin saye da sayarwa.
Kano na da manyan kasuwannin da ake tinkaho da su a Afirka ta yamma da suka hada da Kasuwar Kwari da Kasuwar Kurmi da Kasuwar Sabon Gari da Singer da Kofar Wambai da Kofar Ruwa.
Duk da cewa a yanzu haka akwai dokar kulle a jihar, akwai yiwuwar mutane daga wasu jihohi da ma al'ummar jihar ta Kano yin cudanya da zarar an bude birnin domin bai wa jama'a damar sayen kayan abinci, wani lamari da wasu ke ganin ka iya ta'azzara al'amari.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "A yi gwaji don gano ko coronavirus ce ke hallaka mutane a Kano – Farfesa Usman Yusuf"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?