--
Yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Kano

Yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Kano

Wani abin bakin ciki ya faru a ranar Alhamis yayin da wani yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Rjiyar Lemo, Dan Rimi a jihar Kano.

An tabbatar da mutuwarsa bayan an ciro shi daga cikin ruwan kamar yadda The Nation ta ruwaito. Mai magana da yawun hukumar kashe gobara na jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis. 

Yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Kano Source: UGC 

Ya ce, "Wani Malam Mujittafa Tasiu ne ya kira mu misalin karfe 11.38 na safiyar yana neman dauki kan afkuwar lamarin. "Bayan samun bayanin, mun yi gaggawar tura tawagar ceton mu zuwa wurin da abin ya faru kuma sun isa misalin karfe 11.52 na safe. "Ko da isarsu an tarar cewa Muhammad ya rasu kuma an mika gawarsa ga mai unguwar Danrimi Alhaji Yunusa Yahaya." LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Yaro dan shekara 15 ya mutu a cikin ruwa a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?