--
Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar shiga da fice, Babandede, ya kamu da Coronavirus

Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar shiga da fice, Babandede, ya kamu da Coronavirus


Kwantrola Janar na hukumar shiga da ficen Najeriya, Muhammad Babandede, ya kamu da cutar Coronavirus. Jaridar Punch ta ruwaito. Kwantrolan wanda ya bayyana hakan ta silar sakon Whatsapp da safen nan ya bayyana cewa tuni ya killace kansa tun lokacin da ya dawo daga kasar Birtaniya ranar 22 ga Maris.

Yace, “A yau, an tabbatar na kamu da cutar COVID-19. Tuni na killace kaina tun lokacin da na dawo daga kasar Birtaniya ranar Lahadi 22 na watan nan ta jirgin British Airways a Legas. “Ina kira ga masoyana, jamian hukumar shiga da fice, da yan Najeriya su taimaka min da wadanda suka kamu da addua.” Ya kara da cewa “Lokacine mai wuya amma ba zamu iya canza abinda Allah ya kaddara mana ba.” Babandede ya yi kira da ma’aikatansa su cigaba da bada hadin kai ga mataimakinsa domin ciyar da hukumar gaba.

Babandede Source: UGC A bangare guda, Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane takwas da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya. Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Asabar inda tace: “An tabbatar da mutane takwas sun kamu da #COVID19

a Najerya. 2 a Abuja, 4 a Oyo, 1 a Kaduna, 1 a Osun.“ “Misalin karfe 10:40 na ranar 28 ga Maris, an samu mutane 97 da aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami uku, kuma daya ya rigamu gidan gaskiya.“ Ge jerin bullar a jihohi Lagos- 59 FCT- 16 Ogun- 3 Enugu- 2 Ekiti- 1 Oyo- 7 Edo- 2 Bauchi- 2 Osun-2 Rivers-1 Benue- 1 Kaduna- 1
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar shiga da fice, Babandede, ya kamu da Coronavirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?