
Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 20 sun kamu da cutar Coronavirus, Legas Abuja da Kaduna
Monday, 30 March 2020
Comment
Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane ashirin da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya. Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Litinin inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin sun kamu da #COVID19
a Najerya. 13 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Kaduna, .“ “Dai-dai Karfe 9:o0 na daren 30 ga Maris, mutane 131 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami takwas, kuma biyu ya rigamu gidan gaskiya.“ Ga jerin jiha-jiha Lagos- 81 FCT- 25 Ogun- 3 Enugu- 2 Ekiti- 1 Oyo- 8 Edo- 2 Bauchi- 2 Osun-2 Rivers-1 Benue- 1 Kaduna- 3
Mun kawo muku rahoton cewa Uwargidar Malam Nasir El-Rufai, Hadiza Isma-El-Rufai ta shaidawa Duniya cewa ta ta yi gwajin wannan cuta mai yawo. Amma ba a ji labarin sakamakon ba tukuna.
Hajiya Hadiza Isma-El-Rufai ta yi wannan bayani ne a shafinta na sada zumunta na Tuwita. Mai dakin gwamnan ta kuma godewa addu’o’in da jama’a su ke yi masu. Hadiza El-Rufai ta nuna cewa Gwawnan ya na ta fama da zaman kadaici na kebewa sauran jama’a,
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
b
0 Response to "Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 20 sun kamu da cutar Coronavirus, Legas Abuja da Kaduna "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?