
Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC
Tuesday, 24 March 2020
Comment
- Kyari, wanda shine shugaban ma’aikatan fadar shugaba Buhari na dauke da cutar COVID-19 Wani rahoto da jaridar Daily Sun ta ruwaito ya bayyana cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya killace kansa. Kamar yadda rahoton ya bayyana, shugaban ma’aikatan mataimakin shugaban kasar, Ade Ipaye, wanda shima babban lauya ne,
ya killace kansa. Osinbajo da Kyari dai suna zauna gab da juna ne a taron majalisar zartarwar da aka yi na karshe a fadar shugaban kasar. Sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Covid-19 ya nuna cewa shugaban baya dauke da kwayar cutar kamar yadda Thisday ta ruwaito.
Hukumar NCDC ta sanar da shugaban kasar cewa ba ya dauke da kwayar cutar a safiyar yau a Abuja. A cewar wata majiya daga fadar shugaban kasa, gwajin da aka yi ya nuna cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya kamu da cutar kamar yadda sakamakon ya nuna a ranar Litinin.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Yanzu-yanzu: Osinbajo ya killace kansa bayan ya zauna kusa da Kyari a FEC"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?