
Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya
Monday, 23 March 2020
Comment
Ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki inda yace: "Bisa shawarar kwamitin yakar Coronavirus, shugaba Buhari ya bada umurnin daukan wadannan matakai: i. Dakatad da taron majalisar zantarwa har sai an bukaci hakan ii. Dage zaman masu ruwa da tsaki zuwa ranar Alhamis, 26 ga Maris, 2020 iii. Rufe dukkan iyakokin Najeriya na tsawon makonni hudu daga ranar 23 ga Maris, 2020."
A bangare guda, mai martaba sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad ABubakar ya bada umurnin kulle dukkan Masallatan birnin tarayya Abuja.
Hakazalika Shugabannin Masallacin kasa dake Abuja, sun sanar da dakatad da Sallolin Khamsu-Salawati da Juma'a a Masallacin tare da kulleta domin takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta fara addaban Najeriya. A jawabin da suka saki ranar Litinin, jagorancin Masallacin sun bayyana cewa fari daga yau (23 ga Maris), za'a kulle dukkan shaguna, gidajen abinci,
da kasuwan dake makwabtaka da Masallacin. Jawabin yace: "Dubi ga lamarin kiwon lafiyar kasa ta COVID19, jagororin masallacin kasa ta dakatad da Khamsu-Salawati, Sallar Juma'a, tarurruka, da duk wani ayyuka a Masallacin da harabarta." "Har da Shagunan kasuwanci da gidajen abincin dake jikin Masallacin za'a kulle." "Yayinda zamu cigaba da addu'a ga Allah ya yaye mana wannan annoba kuma ya shiryar damu, muna kira da mutane su bamu hadin kai da fahita kan wannan mataki." LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
0 Response to "Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin Najeriya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?