
Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji
Wednesday, 4 March 2020
Comment
jaridar TheCable ta ruwaito. Daya daga cikin mazauna yankin ya ce sama da sa’a daya, sojoji daga rundunar soji ta brigade 25 a Damboa na ta musayar wuta da yan ta’addan. “Sun zo su da yawa a motocin hilux. Mun gan su kimanin su 20 kafin muka fara gudu cikin daji,” daya daga cikin mazauna yankin da suka tsere.
Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji Source: Facebook
Wani mazaunin kauyen ya bayyana cewa sojojin bataliya ta 117 sun dakile harin a Chibok, amma cewa sun riga da sun sace kayayyakin abinci daga wajen mazauna kauyen da suka far mawa. Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar, Sagir Musa ba kan harin Damboa. Wani soja daga bataliyan ya bayyana cewa dakarun soji a tsaron yankin yayinda suke samun tallafi daga rundunar sojin sama.
“An turo wani jirgin yaki daga rundunar a Maiduguri,” in ji shi. “Don haka a yanzu muna da tallafi daga rundunar sojin sama, kuma muna kora makiyan dga wajen da kuma kare yankin. Wasun su na nan har ynzu amma mun rage karfinsu a yanzu.” LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Yanzu Yanzu: Al’umman Damboa sun tsere yayin da yan Boko Haram ke musayar wuta da sojoji"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?