
Yan sanda sun kama masu asiri 3 da kan mutum a Lagas
Monday, 9 March 2020
Comment
Rundunar yan sandan Najeriya reshen jahar Lagas ta kama wasu mutane uku da ake zargi da cire kan wani mutum daga wani makabarta domin yin asiri dashi. Wani jawabi daga Bala Elkana, kakakin yan sandan jahar Lagas a ranar Lahadi, ya ce yan sanda daga sashi na ‘E’ na Festac ne suka kama masu laifin.
“Mai laifin ya tona cewa bokan ne ya aike shi ya je ya karbo masa kan daga wajen ma’aikacin makabartar. “Bokan ya yi ikirarin cewa ya siyi kan ne daga waje Falana kan naira 10,000. “Bokan ya kan nika kan ne tare da wasu abubuwa wajen hada wa abokan harkarsa magunguna,” in ji Elkana.
Ya bayyana cewa mutum na ukun ya tona cewa ya kan haka kaburbura sannan ya cire kawunan mutane yana siyarwa da bokaye. Ya kuma bayyana cewa ana gudanar da bincike sannan za a tura masu laifin kotu da zaran an kammala. A wani labari na daban, mun ji cewa Jami’an rundunar binciken manyan laifuka na rundunar Yansandan Najeriya,SCIID, sun kaddmar da bincike kan dalilin da ya sabbaba mutuwar wani mutumi dan shekara 49 mai suna Babatunde Ishola.
Ana zargin wata daliba yar shekara 16 mai suna Timilehin Taiwo, diyar abokinsa ne ta kashe shi a lokacin da ya yi kokarin haike mata da nufin yin lalata da ita ta hanyar fyade, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Yan sanda sun kama masu asiri 3 da kan mutum a Lagas "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?