
Yadda takalma suka tona wa wasu 'yan fashi da makami asiri a Zaria
Friday, 20 March 2020
Comment
Wani shaida mai suna Sajan Jamilu Tanimu da ke aiki da ofishin ‘yan sanda a Zaria, ya labarta yadda takalman da aka bari a wajen da aka yi fashi da makami suka tona asrin ‘yan fashin. Tanimu yaa bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin da yake bada shaida a gaban wata kotun majistare da ke Zaria,
Tanimu ya ce mai karar ya bayyana yadda ‘yan fashi suka shiga mishi gida tare da kwashe musu kayayyaki amma sai suka bar takalmansu. Bayan kwanaki tara kuwa sai aka kama Isah na sata a wani gida da ke kusa da na wanda ya kai korafin. “A yayin bincike,
Isah ya bayyana cewa tare suke da Mubarak. Amma kuma daga baya sai suka musanta zargin da ake musu,” yace. Bayan tsananta bincike ne aka gano cewa wadannan takalman mallakin Mubarak ne. Amma kuma har yanzu ba a kama komai ba daga cikin abinda aka sata a hannunsu. Hakazalika, shaidar ya kasa yin bayanin yadda takalman suka kai gidan mai korafin. Alkali Ruqayyat Ummi Ahmed ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Maris don ba wa mai gabatar karar kawo shaidarsa.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Yadda takalma suka tona wa wasu 'yan fashi da makami asiri a Zaria"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?