
Yadda aka ci zarafin Sanusi da iyalansa kafin su bar fada - Lauyansa
Wednesday, 11 March 2020
Comment
Shugaban lauyoyin tubabben sarkin Kano, Abubakar Balarabe Mahmoud, ya yi bayanin yadda Malam Muhammadu Sanusi II da iyalansa suna fuskanci cin zarafi bayan an tube masa rawaninsa. Balarabe Mahmoud, tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya,
Ya ce tsohon gwamnan bankin Najeriya din daga bisani ya samu wasikar da ke bayyana cewa ya gaggauta komawa jihar Nasarawa. Balarabe Mahmoud ya ce, "Mun bukaci sanin cewa ko an kama shi ne kuma muna bukatar ganin shaidar hakan. Amma sai kwamishinan 'yan sandan ya tabbatar mana da cewa ba kama shi aka yi ba. Mun sanar da kwamishinan 'yan sandan cewa wannan ya take hakkinsa da kundun tsarin mulki ya bashi don za a mayar dashi ne babu yardarsa."
"Sarkin ya bayyanawa kwamishinan 'yan sandan cewa abokansa sun turo jirgin da zai daukesa tare da iyalansa zuwa jihar Legas. Kawai yana bukatar tsaro ne a filin jirgin don ya bar garin. Kwamishinan kuwa ya hana hakan tare da tabbatar da cewa umarni ne aka bashi. Za su bar iyalansa su tafi Legas amma shi kuwa za a kaishi Abuja daga nan ya wuce Nasarawa.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Yadda aka ci zarafin Sanusi da iyalansa kafin su bar fada - Lauyansa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?