
Warwas: Man fetur ya yi faduwar da bai taba irinta ba a cikin shekaru 18
Monday, 30 March 2020
Comment
Ana ganin cewa farashin zai kara faduwa kasa da haka saboda har yanzu cutar coronavirus na cigaba da mamaya tare da durkusar da tattalin arzikin mutane da kasashe. "Farashin mai yanzu ya yi matukar wulakantar da yasa babu wata riba da kamfanonin sarrafa man fetur ke samu," a cewar wani kwararren masanin harkokin kasuwancin duniya. "Bukatar man fetur ta matukar dusashe saboda takaita zirga-zirgar mutane da bukatar su nesanta da juna sakamakon bullowar annobar cutar coronavirus," a cewar Giovanni Staunovo, masanin kasuwancin man fetur.
Ana ganin cewa kasashen da ke da arzikin man fetur za su rage yawan adadin danyen man da suke fitar da shi zuwa kasuwar duniya saboda yadda farinjininsa ya sauka da kaso 20% idan aka kwatanta da yadda yake da farinjini a shekarar 2019
Karyewar farashin man fetur ne a kasuwar duniya ya sa gwamnatin Najeriya ta rage N25 a farashin litar mai da ake sayarwa a gidajen man da ke fadin Najeriya.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
b
0 Response to "Warwas: Man fetur ya yi faduwar da bai taba irinta ba a cikin shekaru 18"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?