Wani matashi ya lakadawa kakar shi dukan tsiya saboda fasto ya ce mayya ce (Bidiyo)
Tuesday, 10 March 2020
Comment
- Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta twitter mai suna samitauma ya wallafa wani bidiyo mai cike da tausayi da alhini - Bidiyon na dauke da wani mutum da ke zane kakar shi bayan fasto ya ce mishi mayya ce
- Mawallafin bidiyon yayi Alla-wadai da wannan jika tare da faston da ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya tarwatsasu Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta twitter mai suna samitauma ya wallafa wani bidiyo mai cike da tausayi da alhini. Bidiyon na dauke da wani mutum ne da ke zane kakar shi bayan fasto ya ce mishi mayya ce. Kamar yadda jaridar Information,ng ta ruwaito, ya fada tsohuwar da duka ne ba ji, ba gani da baukatar ta amsa laifinta. A yayin wallafa bidiyon, ya rubuta:
“Kalla yadda wani mutum ke jibgar kakarshi bayan mugun fasto ya ce mayya ce. Ina fatan bai kashe wannan tsohuwar matar ba. Wasu fastocin suna da matsala kuma sun dage sai sun tarwatsa iyalai.”
Ba wannan bane karo na farko da fastoci ke ire-iren hakan ga al'umma. Sannanen abu ne idan aka ce fastocin Najerya da na nahiyar Afrika sun saba cin karensu babu babbaka.
A kwanakin baya, Legit.ng ta ruwaito yadda wani fasto ya hada wani tafki a cikin farfajiyar cocinshi wacce ya kira da tafkin waraka. Faston nan na bari a shiga tafkin ne bayan an biya shi dubu hamsin. Ga marasa halin biyan dubu hamsin kuwa, suna biyan dubu goma don a dibar musu ruwan a gora. Faston ya sanar da mabiyan shi cewa ruwan tafkin na maganin ciwuka kuma yana yaye damuwa da talauci.
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y#WitchKillingPractice— Sam Itauma (@SamItauma) March 8, 2020
Can you imagine this man beating his grandmother consequent upon a pronouncement by his greedy pastor that this hapless, poor woman is a witch?
I hope he hasn't killed this woman yet.Some pastors with blunt conscience are bent on destroying families to... pic.twitter.com/DMvM1WyCXD
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Wani matashi ya lakadawa kakar shi dukan tsiya saboda fasto ya ce mayya ce (Bidiyo) "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?