
Wadume: Kotu ta umurci Buratai da ya mika sojoji da ke cikin lamarin don gurfanar dasu
Monday, 16 March 2020
Comment
Wata babbar kotun tarayya a Abuja a ranar Litinin, 16 ga watan Maris, ta umurci Shugaban hafsan sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai da ya mika sojojin da ake zargi da hannu wajen sakin Hamisu Bala wanda aka fi sani da Wadume bayan jami’an yan snada sun kama shi.
Kotun dai ba ta saurari ta bakin Hamisu Bala Wadume da sauran wadanda ake tuhuma ba, kasancewar sojojin da ake zargin ba su bayyana a kotun ba. A ranar 6 ga watan Agustan bara ne wani ayarin rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da masu satar mutane da 'yan fashi ta yi artabu da wasu sojoji a jihar Taraba da arewa maso gabashi Najeriya.
Hakan ya faru ne lokacin da 'yan sandan, dauke da hamisu Wadume cikin sarka suka ta samma wani shinge da sojojin suka kafa, inda sojojin suka bude musu wata, har wasu daga cikin 'yan sandan suka riga mu gidan gaskiya.
An tattaro sojojin suna cewa agajinsu aka nema da su ceci Wadume kasancewar wasu masu satar mutane ne suka sace shi, yayin da wasu rahotannin ke cewa hedikwatar 'yan sanda da ke jihar Taraba ma ba ta da labarin zuwan 'yan sandan. Amma daga bisani 'yan sandan sun musanta. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Wadume: Kotu ta umurci Buratai da ya mika sojoji da ke cikin lamarin don gurfanar dasu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?