Tsugunno bata qareba: Tsohon sarki Sanusi II ya garzaya Kotu
Tuesday, 10 March 2020
Comment
Tsohon Sarkin Kano da aka sauke daga kan kujerarsa a ranar Litinin, Sanusi Lamido, ya lashi takobin bin hakkinsa a kotu domin kalubalantar tsige shi da kuma kange shi a wani wuri da sunan gudun hijira. Lauyan sarki Sanusi, Abubakar Mahmoud (SAN), ne ya bayyana hakan da yammacin yau, Talata,
yayin gana wa da manema labarai a Abuja. Lauyan ya ce sauke Sanusi da tsare shi a wata mafaka sun saba wa doka tare da take hakkinsa na bil'adama. A ranar Litinin ne gwamnatin Kano, ta bakin Usman Alhaji, sakataren gwamnatin jiha, ta sanar da sauke Sanusi II daga kujerar sarkin Kano bisa zarginsa da rashin biyayya ga sabbin dokokin masarautun jihar Kano da aka kirkira a karshen shekarar 2019.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI

0 Response to "Tsugunno bata qareba: Tsohon sarki Sanusi II ya garzaya Kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?