
Ta gujeni da aka koreni daga aiki, yanzu kuma tana so ta dawo bayan na samu kudi
Saturday, 14 March 2020
Comment
Wani mutumi mai suna Jimoh Kazeem yana neman shawara a wajen al'umma akan wata matsala da take damunsa matuka
Sai dai kuma cikin ikon Allah, bayan watanni shida da faruwar wannan lamari wajen da yake aikin suka kira shi suna bashi hakuri akan cewa kuskurene ya sanya suka kore shi ba, inda har suka bashi kyautar naira miliyan sha biyar a matsayin toshiyar baki.
Matarsa na jin wannan abu da ya faru dashi, sai ta fara neman shi tana bashi hakuri akan ya yafe mata tana so ta dawo.
Ga dai rubutun da yayi a shafin nasa na Facebook cikin harshen Turanci:
"Shekaruna 26, amaryata kuma shekarunta 28, mun yi aure shekarar da ta gabata, amma bayan auren mu sai na rasa aikina hakan ya saka matata ta gudu ta barni, bayan mako daya ta dawo ta kwashe komai na gidan, na cigaba da rayuwa haka ni daya, ina bacci a kasa na tsawon watanni shida.
"Kawai watarana sai na samun kiran waya daga wajen dana yi aiki, aka bayyana mini cewa kuskurene ya sanya aka kore ni da laifin cewa na saci kudi, yanzu an kama barawon, saboda haka za a mayar dani bakin aiki, sannan kamfanin zai biyani duka albashin dana rasa a baya da kuma alawus.
"Lokacin dana koma wajen aiki an bani kudi naira miliyan goma sha biyar (N15,000,000) a matsayin albashi da alawus dina. Yanzu matsalar shine matata na son ta dawo bayan taji cewa na samu wannan kudi kuma na koma aiki.
"Shin wace shawara zaku bani, na saketa ne ko kuma na dawo da ita?LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Ta gujeni da aka koreni daga aiki, yanzu kuma tana so ta dawo bayan na samu kudi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?