--
Subahanallah-: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas

Subahanallah-: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas

Wani lebura ya mutu a daren ranar Asabar sakamakon rushewa da ginin Bankin Keystone da ke Palmgroove ya yi a Legas. The Nation ta ruwaito cewa ana yi wa ginin benen da ke Ikorodu Road kwaskwarima ne a lokacin da ya rufto. Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 7.20 na yamma. 

Subahanallah-: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas Source: Twitter 

A lokacin rubuta wannan rahoton, jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Legas (LESEMA), Yan sanda da jami'an hukumar kula da gine-gine na jihar Legas (LABSCA) sun isa wurin.
Kazalika, jami'an hukumar kashe gobara sun isa wurin da abin ya faru domin dauke gawar mammacin tare da killace wurin. Ku biyo mu domin samun cikakken rahoto.




LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Subahanallah-: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?