
Sautin murya: Abinda Sheikh Dahiru Bauchi ya fada a kan tube rawanin Sanusi II
Wednesday, 11 March 2020
Comment
A yayin da jama'a ke cigaba da bayyana mabanbantan ra'ayoyi a kan tsige Muahammadu Sanusi II daga kujerar sarkin Kano, babban malamin darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya tofa albarkacin bakinsa.
A wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na radiyon BBC, Sheikh Dahiru Bauchi, ya ce tun bayan samun sanarwar tube Sanusi II, suke aika sako ga magoya bayansu a kan su kwantar da hankalinsu, kar su tashi hankalinsu a kan abinda ya faru.
A cewar, babban malamin, wuta da kudi suna hannun gwamnta, a saboda haka zasu iya daukan mataki marar dadi a kan wadanda suka fito domin nuna rashin jin dadinsu.
Sheikh Dahiru Bauchi ya yi addu'a ga tsohon Sarki Sanusi tare da yi masa fatan alheri a rayuwa.
"Su suke da wuta a hannusu, su suke da kudi a hannunsu, zasu iya bayar da umarnin a harbe mutane. Babu gwamnati a hannunmu, a saboda haka babu wanda zai saurare mu," a cewar Sheikh Dahiru.
Sannan ya cigaba da cewa, "a kwantar da hankali, kar a tayar da hankali, a cigaba da addu'a, gara a yi shiru, Allah zai yi mana sakayya."
Saurari Sautin Muryar Shehin Malamin Anan👇👇👇👇
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YSaurari martanin Sheikh Dahiru Usman Bauchi a kan sauke Sarki Muhammadu Sanusi II 👇#SanusiLamido pic.twitter.com/TqMVAdc9NG— BBC News Hausa (@bbchausa) March 10, 2020
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Sautin murya: Abinda Sheikh Dahiru Bauchi ya fada a kan tube rawanin Sanusi II"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?