
Sanusi II: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari
Wednesday, 11 March 2020
Comment
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya kwatanta zargin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na da hannu wajen tube rawanin Muhammadu Sanusi II, da zance mara tushe balle makama.
Amma kuma, a martanin gaggawa da Ganduje yayi ta takardar da sakataren yada labarai, Abba Anwar ya fitar, ya ce tube rawanin basaraken hakkin gwamnatin jihar ne kuma hakan ta faru ne saboda gamsassun dalilai.
Kamar yadda gwamnan ya sanar, Sanusi ya take bangare na uku, sashi na 13 na dokokin masarautar jihar Kano din na 2019. Wanda kuwa idan ba a dau matakin gaggawa ba, zai iya bata sunan masarautar Kano din baki daya.
“Wannan dokar ta jihar Kano ce ba ta gwamnatin tarayya ba. A don haka ne babu dalilin danganta wannan horarwar da wani sashi da ya wuce gwamnatin jihar.” Ya kalubalanta.
“A don haka ne nake mamakin yadda wani zai fito kwatsam daga wani waje ya fara zargin fadar shugaban kasa da hannu wajen tubr rawanin Muhammadu Sanusi. Dalilan tube masa rawani kuwa a bayyane yake,” Gwamnan ya kara da cewa.
Gwamnan ya kara da jaddada cewa duk wanda ya danganta lamarin da fadar shugaban kasa, toh yana da wata manufa ko kuma kwata-kwata baya son gaskiya.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Sanusi II: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso a kan zargin sa hannun Buhari"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?