
Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta
Thursday, 12 March 2020
Comment
- Sabon Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya koma gidan sarauta a daren ranar Laraba, 11 ga watan Maris - Bayero ya shiga Soron Shekara sannan daga nan ya shiga Soron Ingila, wanda nan ne gidansa a cikin masarautar inda ya ke karban gaisuwa daga ahlin gidan sarauta da sauran sarakunan gargajiya
Daruruwan al’umman Kano sun isa gidan sarautar domin shaida al’ada na shigar sarki gidan sarautar ta wata kofar tarihi, wacce ta ke al’ada da ke tabbatar da daura Bayero a matsayin sarki.
Za kuma a gudanar da hawan daba na musamman domin karrama sarkin, tare da addu’o’i na musamman don zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?