--
Nayi imani da Allah cewa a yanzu aka hadani da mai cutar Coronavirus zai warke - Matashin mai magani dan Kano

Nayi imani da Allah cewa a yanzu aka hadani da mai cutar Coronavirus zai warke - Matashin mai magani dan Kano



A yayin da duniya baki daya ta rude, masana kimiyya suka bazama neman maganin wannan cuta ta kafewar numfashi, an sami wani matashin mai magani a Kano mai suna Malami Jan Wuya, da ya bugi kirji yace shi yana da maganin wannan cuta Koda yake wasu mutanen na gani cewa zancen nasa yafi kama da shiririta,

amma wasu daidaikun mutane na ganin cewa zai fi kyau a bashi dama ya gwada baiwar da Allah yayi masa. Da aka tambayeshi shin ko ya taba ganin mai cutar a zahiri, sai ya ce: "Nan fa daya, bai taba gani ba," amma ya hakikance da gwamnati za ta kira shi zai nuna irin tashi basirar da Allah yayi masa.

Ga dai abinda ya ce: "Assalamu Alaikum, yana da kyau dukkanin Musulmai su sani cewar kowacce irin cuta da take a duniya, ba ta sauko ba sai da aka fara saukar da maganinta.

"Saboda haka dan mutum ya fito ya ce yana da maganin wannan cuta ta Coronavirus ba sabon abu bane ba kuma abin mamaki bane. "Allah ne ya huwace mini, nayi imani da ikon Allah a yanzu aka hadani da mai Coronavirus zai warke. "Ban taba gwada maganin a jikin kowa ba, hasalima ban taba ganin mai cutar ba, amma na tabbata yanzu aka hadani da mai cutar zan warkar dashi. "Saboda haka nake kira ga gwamnatin Najeriya dama sauran kasashen duniya baki daya da su kirani su bani dama na gwada bajintar da Allah yayi mini.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

Related Posts

0 Response to "Nayi imani da Allah cewa a yanzu aka hadani da mai cutar Coronavirus zai warke - Matashin mai magani dan Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?