
Najeriya: An Bada Umurnin Yin Amfani Da Miliyan 620 Don Dakile Cutar Coronavirus
Saturday, 7 March 2020
Comment
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya jagoranci wata tawaga da ta kunshi wasu abokanan aikinsa kai ziyarar ganin irin matakan da gwamnati ke dauka na samun wurin killace duk wani da aka samu da cutar Coronavirus.
Tawagar ta yi tattaki ne zuwa babban asibitin gwamnati dake Gwagwalada a Abuja, babban birnin tarayyar kasar inda ake aikin gina wuraren killacewar.
Shugaban majalisar ya nuna bacin ransa ganin yadda aikin ke tafiyar hawainiya. Ya kuma ba Ministar Kudi, Zainab Shamsunah Ahmed umurnin ta yi gaggawar sakin kudi kimanin Naira Miliyan 620 ga Cibiyar Kula Da Cututtuka ta kasar, saboda a gaggauta kammala aikin, duk da cewa har yanzu ba a samu wani wanda ya kamu da cutar ba, bayan dan asalin kasar Italiyar nan da ya shigo Najeriya da cutar, wanda aka killace a wani asibiti dake jihar Legas.
A bangaren Majalisar wakilai kuma, mahawara ce ta kaure akan cutar Coronavirus inda a karshe majalisar ta yi amai ta kuma lashe akan batun zuwan su hutu saboda bullar cutar, har ma ta ce ta janye batun zuwa hutun saboda korafe korafen al’umma, a cewar dan Majalisa Sada Soli Jibiya.
Dan majalisar ya kara da cewa wasu kasashe irin su China, Japan, Hong Kong da Iran sun rufe Majalisun su, amma su ba za su tafi hutu ba saboda kar a kawo rudani a cikin kasa.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Najeriya: An Bada Umurnin Yin Amfani Da Miliyan 620 Don Dakile Cutar Coronavirus"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?