
Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda
Monday, 9 March 2020
Comment
Dan kwallon Najeriya, Chineme Martins dake tsaron gida a kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United ya yanke jiki ya fadi, daga nan ya sheka barzahu a yayin da yake tsaka da taka leda. Jaridar Daily Trust ta ruwaito dan kwallon ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da kungiyarsa ta Nassarawa United ke karawa da kungiyar Katsina United, a filin wasa na Lafia dake jahar Nassarawa a ranar Lahadi, 8 ga watan Maris.

Inji shi. Ita ma hukumar shirya gasar firimiya ta Najeriya, ta tabbatar da mutuwar Chineme, kuma ta yi alkawarin ganin an gudanar da bincike a kan gawarsa domin tabbatar da musabbabin mutuwar tasa. “Muna fatan sakamakon binciken da za mu gudanar zai bamu haske game da matakin da ya kamata mu dauka a gaba idan har bamu da tsarin a yanzu.”
Inji ta. Haka zalika hukumar ta ce za ta cigaba da tuntubar kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United tare da iyalan mamacin don sanin hanyoyin da suka fi dacewa su basu tallafi da gudunmuwa a wannan lokaci da suke jimami da alhini.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?