
Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2
Wednesday, 25 March 2020
Comment
- Yanzu mutane da ke dauke da coronavirus a Najeriya sun kai 46 bayan an sake samun sabbin mutane biyu
Ta wallafa: “An tabbatar da sabbin lamuran #COVID19 a Najeriya: 1 a Lagas sannan 1 a Osun. “Dukaninsu sun kasance matafiya da suka dawo Najeriya cikin kwanaki 7 da suka gabata.
“Da misalin karfe 07:00 na safiyar ranar 25 ga watan Maris, an tabbatar da masu dauke da #COVID19 46 a Najeriya. An sallami mutane 2 sannan mutum 1 ya mutu.” A bangare guda mun ji cewa Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya bukaci jama'ar jiharsa da kada su ji tsoro a kan kebancesa da aka yi sakamakon cutar coronavirus da ya kamu da ita. A ranar Talata ne dai aka tabbatar da cewa gwamnan na dauke da cutar coronavirus din. Mohammed ya killace kansa tun bayan da yayi hannu da dan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, wanda aka gano yana dauke da cutar, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?