Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus
Monday, 30 March 2020
Comment
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar coronavirus a kasar. Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya sanar da hakan a ranar Litinin, 30 ga watan Maris, a lokacin taron tawagar fadar Shugaban kasa kan cutar Covid-19 a Abuja, babbar birnin kasar, Channels TV ta ruwaito. Ya ce: “Zuwa yanzu, an salami mutum uku bayan sun warke. Amma abun bakin ciki, an kara rasa rai a karshen mako sakamakon mummunan yanayi na rashin lafiya da mara lafiyan ya shiga.
Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus Source: UGC “Mun jajirce wajen gano wadanda suka yi tarayya kuma manufamu shine hanyar shawo kan lamarin cikin gaggawa, killace su da kuma bibiyar wadanda suka yi tarayya dasu sannan suma a killace su da kuma yi masu magani, domin rage yaduwar cutar.”
“A yau 30 ga watan Maris, 2020, mun samu mutane 111 da aka tabbatar suna dauke da Covid-19 a Najeriya wadanda 68 suka kasance a Lagas, 21 a babbar birnin tarayya, bakwai a Oyo, uku a Ogun, biyu a Bauchi,biyu a Edo, biyu a Osun, biyu a Enugu, sannan daddaya a Benue, Ekiti, da Rivers." Ya kara da cewa Najeriya ta tabbatar da masu coronavirus 111, cewa mafi akasarinsu wadanda suka dawo daga kasashen waje ne. A cewar ministan lafiyan,
an fi samun yawan wadanda suka kamu a Lagas da Abuja ne saboda sune ,manyan kofofin shigowa kasar. Ehanire ya gargadi yan Najeriya da su kare tsoffi a cikinsu, da wadanda ke fama da lalura ta rashin lafiya domin sune suke cikin mafi hatsari. A baya mun ji cewa gwamnatin jihar Legas ta sallam wasu mutane biyar daga cibiyar killacewa da ke asibitin cututtuka masu yaduwa a unguwar Yaba bayan an tabbatar da cewa yanzu basa dauke da kwayar cutar coronavirus.
Ya zuwa yanzu an sallami jimillar mutane 8 kenan daga cibiyar. Mutanen da aka sallama suna cikin koshin lafiya, babu alamar gajiya ko damuwa a tare da su, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
b

0 Response to "Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?