
Ku kyale asibitoci masu zaman kansu su gudanar da gwajin Coronavirus – Dangote ga FG
Thursday, 26 March 2020
Comment
watau Coronavirus. A cewar Dangote, idan gwamnati ta bayar da wannan dama, hakan zai rage tsawon lokacin da aka dauka kafin fitowar sakamakon gwajin cutar, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shi.
Dangote ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 25 ga watan Maris a jahar Legas inda yace: “A yanzu cibiyoyin gwaje gwaje guda biyar ne kacal na gwamnati dake gudanar da gwaje gwaje a duk fadin Najeriya, duk kuwa da cewa muna da cibiyoyi masu kyau da ka iya gudanar da wannan gwaji, amma basu samu amincewar gwamnati ba.”
da kuma kulawa dasu. “Muna kara samar da cibiyar Coronavirus guda daya a Victoria Island Legas, za kuma mu dauko hayar kwararru daga sassan duniya domin taimaka ma jami’an kiwon lafiyarmu tare da horas da su. “COVID-19 ta shafemu duka, kuma tana barazana ga kiwon lafiyarmu, tattalin arzikinmu, zamantakewarmu da kuma walwalarmu, don haka akwai bukatar hada kai domin yakar wannan makiyinmu.”
Inji shi. Daga karshe Dangote ya bayyana cewa za su gudanar da ayyukan cikin lokaci domin samun biyan bukata. Sauran kamfanonin dake cikin wannan hadaka sun hada da Zenith Bank, Guaranty Trust Banka, MTN, ITB da sauransu.
A wani labarin kuma, karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Ramatu Aliyu ta bayyana cewa ta hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta gudanar da gwajin annobar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus a kanta.
Ramatu ta bayyana cewa ta yi mu’amala da mutanen da gwaji ya tabbatar da cewa suna dauke da cutar, hakan ne yasa wajibi ita ma ta yi wannan gwaji domin sanin matsayinta. Zuwa yanzu dai hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta bayyana cewa daga cikin mutane 46 da aka samu suna dauke da cutar Corona,
mutane 8 a babban birnin tarayya Abuja su ke, daga cikinsu har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abb Kyari. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Ku kyale asibitoci masu zaman kansu su gudanar da gwajin Coronavirus – Dangote ga FG "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?