Ku barni na dauki diyata ta mutu a gabana - Magidanci ya nemi gwamnati ta bashi 'yarshi bayan yaga wajen da ake kula da su bai da kyau
Tuesday, 31 March 2020
Comment
- Wani fusataccen mahaifin ya bayyana halin da diyar shi ke ciki a wata cibiyar killace masu cutuka masu yaduwa - Duk da dattijon bai sanar da sunan wacce cibiyar bace, ya ce tunda aka kai diyar shi sun ki kulata duk da an gano tana dauke da Coronavirus
- A cewar mahaifin, hatta abinci an hana ta kuma babu likita ko ma'aikaciyar jinyar da ta duba ta tun zuwansu sai cewa da ake musu su tafi gida Wani bidiyon dattijon mutum wanda aka gano mahaifin wata yarinya ce da aka killace a cibiyar killace cutuka masu yaduwa ya mamaye yanar gizo. An ga dattijon na korafi cike da kunar rai a kan halin da diyar shi ke ciki.
Mutumin da ya bayyana sunan shi da Olanutu, ya sanar da manema labarai ne yayin da ake tattaunawa da shi cewa an gano diyar shi na dauke da cutar coronavirus. An kuma bar ta ba a kula da ita a daya daga cikin cibiyoyin killace masu jinyar cutuka masu yaduwa kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
Duk da bai bayyana sunan cibiyar ba, fusataccen mahaifin ya ce an bar diyar shi babu abinci tun bayan da aka kawo ta cibiyar. "Ministar ta zo da kanta ta ga abinda yake faruwa. Ba karya nake yi ba. Sunana Olanutu. Me suke yi a nan? Tun safe bata ga likita ba ko ma'aikaciyar jinya. Ba a ciyar da ita ba kuma suna cewa in dauketa. Bari muje gida kawai ta mutu a can tunda babu wanda ya damu da ita. Idan tana dauke da cutar ba yana nufin ta samu lasisin mutuwa bane" ya ce.
LATSA NANπππ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
b

0 Response to "Ku barni na dauki diyata ta mutu a gabana - Magidanci ya nemi gwamnati ta bashi 'yarshi bayan yaga wajen da ake kula da su bai da kyau "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?