
Ina samun N1m a kowanne wata daga siyar da abubuwan ci a titin Legas - Okorafor
Saturday, 7 March 2020
Comment
- A wajen Chinedu Okafor, talla dai ta zama wani abu da ya kawo sauyi a rayuwar shi
- Dan Najeriyan da ya koma jihar Legas din a 2016 ya fara talla ne a cunkoson kan titin jihar
Kamar Yanda Jaridar Legit.ng ta rawaito ta gano cewa, dan kasuwar ya dauka matasa 12 aiki wadanda ya taho dasu daga kauyensu don taimaka mishi wajen talla a titin. Okorafor ya fara basu kayan da suka hada da gala da kuma lemukan inda yake basu kashe 30 na ribar da suka samu a ranar.
Ina samun N1m a kowanne wata daga siyar da abubuwan ci a titin Legas - Okorafor Source: Original
Joseph ya ce: “A yayin cika musu burikansu na samun abun kashewa, yana biya musu kudin haya tare da hada musu cin abincin dare akai-akai.” Kamar yadda Joseph ya sanar, Chinedu bai daina hawa kan titin ba ko bayan da yake ba samarin kayan na siyarwa. Sau da yawa yana zuwa tallar tare da su ne. A karshen 2018,
Wanda ya cika shekaru biyu cif da zuwan shi jihar Legas, yana da a kalla matasa 100 da ke siyar mishi da kayayyaki a kan titunan jihar. Akwai kuma masu sarin da ke siya daga wajen shi. Daga nan ne ya kara buda kasuwancin shi inda ya koma siyar da biskit, ruwan lemu da kuma dankali soyayye.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Ina samun N1m a kowanne wata daga siyar da abubuwan ci a titin Legas - Okorafor "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?