
Hotunan wasu yan gida daya su 4 da suka mutu a cikin barci
Wednesday, 25 March 2020
Comment
- Wata mai suna Nkiru Chukwuemeka Unachukwu ce ta sanar da labarin a shafin Facebook Yayinda yan Najeriya ke ci gaba da gwagwarmaya da annobar da ake ciki a yanzu, abubuwan bakin ciki na ci gaba da faruwa a fadin kasar.
Kwanan nan ne aka rahoto cewa wasu iyalai su hudu sun mutu a cikin barcinsu. Wata mai amfani da shafin Facebook, Nkiru Chukwuemeka Unachukwu ce ta watsa labarin. Iyalan wadanda suka hada da ma’auratan da yaransu kanana su biyu, sun kwanta barci ne inda basu kara tashi ba. An dauki hoton gawarwakin iyalan a kan gado, a yanayin da suka kwanta barcin, illa gawar mahaifin wanda rabin cikinsa na a kan gado sannan rabi na a kasa.
“Na kasa yarda ta yaya za a yi iyalai guda ba tare da ciwon komai ba a ce miji, mata da yara biyu su kwanta barci a daren jiya amma su kasa tashi da safe. Akwai hannun shaidan a ciki. Allah ya ji kanku,” Unachukwu ta rubuta. KU
Majiya daga fadar shugaban kasan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa an shawarci dukkan mutanen da suka yi hulda da Abba Kyari. Ya ce ana kyautata zaton cewa hakan yasa ma'aikatan fadar shugaban kasa basu zo aiki yau ba. Bugu da kari, dukkan ma'aikatan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, basu shiga fadar ba a yau illa mai magana da yawunsa. A yanzu dai, da alamun ana shirin kulle fadar shugaban kasar saboda an umurci dukkan dukkan ma'aikatan su koma gida.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Hotunan wasu yan gida daya su 4 da suka mutu a cikin barci "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?