
Gwamnan Kano ya kama motar da ta shigo Kano bayan rufe iyakoki saboda annoba
Tuesday, 31 March 2020
Comment

Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya ci karo da wata katuwar mota da ta nemi shigowa jihar Kano bayan an rufe iyakokin shiga jihar. Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi ram da wannan mota ne sa’ilin da ya fito wani kewaye a Ranar Litinin, 30 ga Watan Maris, 2020,
kamar yadda mu ka ji labari. Darektan harkokin yada labarai na gwamnatin Kano, Salihu Tanko Yakassai ne ya bayyana wannan a shafinsa na Tuwita, inda ya wallafa bidiyon haduwar. Wannan gingimari wanda ta ke cike da jama’a ta yi kokarin shigowa cikin Kano ne duk da gwamnatin jihar ta garkame iyakokinta saboda annobar COVID-19. Salihu Tanko Yakassai ya bayyana cewa Tawagar gwamnan ta raka wadannan mutane da aka kama zuwa ofishin ‘Yan Sandan da ya fi kusa domin a hukuntasu.
H.E @GovUmarGanduje on an inspection of Kano borders, intercepted a truck load of people from Madalla in Abuja, enroute to Kano despite the closure of Kano borders. The Governor personally escorted the truck to the nearest police station for the law to take its cause. pic.twitter.com/uuKfRxk1W1— Peacock (@dawisu) March 30, 2020
A wannan bidiyo an ji Mai girma gwamna Abdullahi Ganduje ya na tsawatawa Direban motar yayin da wadanda aka dauko a motar su kayi ta yi wa gwamnan shewa. Direban wannan mota ya fadawa gwamnan Kano cewa sun fito ne daga Garin Madalla da ke cikin karamar hukumar Suleja a Neja, kusa da babban birnin tarayya Abuja. Gwamnan da Tawagarsa su na sanye da safar hannu domin gudun kamuwa da cutar Coronavirus.
Sai dai da alamu gwamnan bai rufe fuskarsa da tsummar kariya ba. Kawo yanzu babu wanda ya kamu da wannan cuta ta COVID-19 a jihar Kano mai tarin jama’a. Gwamnatin Ganduje ta na cigaba da kokarin kare rayukan al’umma.
Ganduje ya kama motocin da suka yi yunkurin shiga Kano— BBC News Hausa (@bbchausa) March 30, 2020
π https://t.co/2WnudcFQEI pic.twitter.com/7yFNXlT87e
LATSA NANπππ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
b
0 Response to "Gwamnan Kano ya kama motar da ta shigo Kano bayan rufe iyakoki saboda annoba"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?