
Gwaji ya nuna Gwamna Seyi Makinde ya na dauke da kwayar COVID-19
Monday, 30 March 2020
Comment
“Yanzu na samu labarin gwajin cutar COVID-19 da na yi. Ina dauke da cutar. Alamomin ciwon ba su fara bayyana a kai na tukuna ba tukuna.” Injiniya Makinde ya kuma kara da cewa: “Zan cigaba da kebe kai na daga bainar jama’a.” Gwamnan ya bayyana wannan ne da karfe 6:04 na yamman Litinin. Gwamnan ya bayyana cewa ya nada tsohon shugaban asibitin koyar da aiki na jami’ar Ibadan, Temitope Alonge a matsayin shugaban kwamitin yaki da cutar a Oyo.
Farfesa Temitope Alonge shi ne zai jagoranci wannan kwamiti da za su yi aikin ganin bayan annobar Coronavirus, yayin da gwamnan ya ke faman jinya a jihar. A jawabin gwamna Seyi Makinde, ya yi kira ga mutanensa su cigaba da bin sharudan da aka kafa na cewa kowa ya tsaya a cikin gida, domin a rage yaduwar annobar. A halin yanzu masu dauke da wannan cuta a Najeriya sun haura mutane 100.I just received my COVID-19 confirmation test result. It is POSITIVE. I am asymptomatic and will continue to self-isolate. pic.twitter.com/SX6UAYBb0S— Seyi Makinde (@seyiamakinde) March 30, 2020
Rahotannin da mu ka samu daga hukumar NCDC shi ne cutar ta kashe mutane biyu yanzu. Da wannan sakamako da aka bayyana da yamman nan, gwamnonin da ke dauke da COVID-19 a kasar nan sun zama uku, bayan Nasir El-Rufai da kuma Bala Mohammed.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
b
0 Response to "Gwaji ya nuna Gwamna Seyi Makinde ya na dauke da kwayar COVID-19 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?