
Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi
Friday, 13 March 2020
Comment
- Fadar shugaban kasa tayi martani a kan zargin kaiwa shugaban kasa Muhammad Buhari hari da aka yi a jihar Kebbi
Wani bidiyo dai ya bayyana inda wani matashi ke ta kokarin cafko shugaban kasa Muhammadu Buhari a bikin baje kolin kamun kifi da aka yi a jihar Kebbi. Wannan bidiyon kuwa ya jawo cece-kuce daga wajen ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani.
A wata takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, ya ce matashin dai masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ba harar shi yayi niyya ba. "Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kebbi a ranar Alhamis don bude taron bikin baje kolin kamun kifi da al'adun gargajiya na jihar Kebbi.
Yayi kokarin kaiwa garesa." Ya kara da cewa, "Sanannen abu ne cewa hakan ba za ta yuwu ba. Jami'an tsaro kuwa sun hana matashi kaiwa gareshi wanda yasa matashin ya dinga kara yunkuri. A halin yanzu manyan 'yan adawa na cewa harar shugaban kasar yayi niyya. Makiya sun saba juya abun alheri zuwa sharri. Amma kansu suke ba haushi don kullum kasar na samu ci gaba,"
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?