
Dalilinmu na gayyato dan kasar Italiya mai cutar 'Corona Virus' Najeriya - Kamfanin Lafarge
Sunday, 1 March 2020
Comment

A yayin da cutar 'Corona Virus' ke cigaba da shiga kasashen duniya, kamfanin siminti na 'Lafarge Africa Pls' da ke jihar Ogun ya bayyana dalilinsa na gayyato baturen kasar Italy da aka gano cewa yana dauke da kwayar cutar. A jawabin da darekta a kamfanin, Segun Soyoye, ya fitar ya bayyana cewa sun gayyaci baturen zuwa kamfanin ne domin duba yadda aka kafa wasu injina da aka sayo daga kasar Sweden.
Jami'an gwamnati sun bayyana cewa ya zuwa yanzu akwai mutane 39 da aka kebe su a wata cibiya domin duba lafiyarsu bayan an tabbatar da cewa sun gana da baturen bayan zuwansa Najeriya.LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Dalilinmu na gayyato dan kasar Italiya mai cutar 'Corona Virus' Najeriya - Kamfanin Lafarge "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?