
COVID-19: Sabbin mutum 11 sun kamu a Najeriya, jimilla 81
Saturday, 28 March 2020
Comment
Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta kara tabbatar da sabbin mutane 11 da suka kamu ta kwayar cutar Covid-19 wato coronavirus a kasar. An samu karuwar mutane takwas ne a Legas sannan guda biyu a Enugu sai kuma daya a jihar Edo. Hakkan na nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar a halin yanzu ya kai 81.
A cewar hukumar ta NCDC, "an samu sabbin mutane 11 da suka kamu da Covid-19 a Najeriya; 8 a jihar Legas, 2 a Enugu da kuma guda daya a jihar Edo kawo yanzu a ranar 27 ga watan Maris na 2020 misalin karfe 11.55 na dare, jimlar wanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar 81. An sallami mutane 3 sai kuma mutum daya ya mutu."11 new cases of #COVID19 have been reported in Nigeria: 8 in Lagos, 2 in Enugu & 1 in Edo State— NCDC (@NCDCgov) March 27, 2020
As at 11:55pm 27th March, there are 81 confirmed cases of #COVID19 reported in Nigeria. 3 have been discharged with 1 death. pic.twitter.com/7p3v3qAcGM
Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane fiye da 15,000 a fadin duniya. Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, sannan an sallami mutane biyu da suka warke bayan sun sha magungun a cibiyar da aka killace su, kamar yadda kididdigar NCDC ta nuna. Yawacin mutanen da aka samu da kwayar cutar corona a Najeriya,
'yan kasa ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai. An tabbatar da samun kwayar cutar a jikin manyan jami'an gwamnati guda uku ciki har da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin shugaban kasa Abba Kyari da a halin yanzu yana samun kulawa daga likitoci.As at 11:55pm 27th March, there are— NCDC (@NCDCgov) March 27, 2020
81 confirmed cases
3 discharged
1 death
For a breakdown of cases by states in real time, please see https://t.co/zQrpNeOfet
Currently;
Lagos- 52
FCT- 14
Ogun- 3
Ekiti- 1
Oyo- 3
Edo- 2
Bauchi- 2
Osun-1
Rivers-1
Enugu- 2#COVID19NIGERIA
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
b
0 Response to "COVID-19: Sabbin mutum 11 sun kamu a Najeriya, jimilla 81 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?