--
COVID-19: abinda Dangote ya fada bayan sakamakon gwajinsa ya fito

COVID-19: abinda Dangote ya fada bayan sakamakon gwajinsa ya fito



Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya sanar da cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar COVID-19. An ji tsoton cewa Dangote zai iya kamuwa da kwayar cutar coronavirus bayan ya yi mu'amala da Abba Kyari,

shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da aka tabbatar da cewa yana dauke da kwayar cutar. A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Dangote ya bayyana cewa ya yi gwajin ne a matsayinsa na dan kasashe da dama sannan shugaba a kasuwanci. Ya ce yana jagorantar shugabannin a bangaren kasuwanci domin taimakon gwamnati a kokarinta na dakile yaduwar cutar. Dangote ya bayyana cewar annobar cutar coronavirus ta taba lafiyar jama'a da sauran harkokinsu.





 A ranar Lahadi ne kasar Andolus (Spain) ta sanar da mutuwar mutane 838 sakamakon kamuwa da kwayar cutar coronavirus.

Ya zuwa yanzu, kwayar cutar coronavirus ta kashe mutane fiye da 30,000 a fadin duniya a karshen makon nan. Kwayar cutar ta fi gigita kasar Amurka da yankin nahiyar turai a 'yan kwanakin baya bayan nan.

A wata kididdiga da jami'ar 'Johns Hopkins' ta gudanar, ta bayyana cewa mutane 30,800 ne kwayar cutar COVID-19 ta halllaka a fadin duniya, yayin da take cigaba da mamaya da karya tattalin arzikin mutane da na kasashe. Mutane fiye da 20,000 ne kwayar cutar ta hallaka a iya yankin nahiyar turai. Kwayar cutar ta kashe mutane fiye da 1400 a rana daya a kasar Spain da Italy.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "COVID-19: abinda Dangote ya fada bayan sakamakon gwajinsa ya fito "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?