Coronavirus: Za a fara koyar da dalibai karatu ta gidan rediyo da gidan talabijin a jihar Legas
Friday, 20 March 2020
Comment
- Gwamnatin jihar Legas ta bayyana kudurinta na fara koyar da dalibai darasi ta gidajen rediyo da talabijin - Gwamnati ta dauki wannan mataki ne bayan dakatar da makarantu da tayi sanadiyyar bullar cutar Corona a Najeriya
- Wannan sabon tsari na koyarwa zai shafi iya daliban ajin karshe ne na sakandare, wadanda za su rubuta jarrabawar WAEC Kwamishinar ilimi ta jihar Legas, Mrs. Folasade Adefisayo, ta bayyana cewa sun fara gabatar da shirye-shirye da za a dinga koyarwa da daliban sakandare da suke ajin karshe darasi ta gidan rediyo da gidan talabijin.
A wata hira da tayi da LTV a Legas yau Juma'a, kwamishinar ta ce malaman makaranta za su dauki sautin darasin da suke koyawa dalibai guda takwas za a sanya su a gidajen rediyi da gidajen talabijin da kuma yanar gizo.
Jerin darasin da za su koyar sun hada da English Language, Mathematics, Biology, Chemistry, Physics, Literature In English, Financial Accounting da kuma Economics. Folashade wacce ta shawarci makarantu gwamnati dana kudi da su bi dokar da aka saka ta rufe makarantu, ta kara da cewa:
"Kun san a makarantun mu da akwai yara da dama, kuma yara babu wanda ya isa ya hanasu wasa da junansu. "Saboda haka mun saka dokar ne domin mu kare yaran mu, mun yadda kowacce makaranta ta rufe koyar da karatu har zuwa lokacin da zamu sanar a bude." LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI

0 Response to "Coronavirus: Za a fara koyar da dalibai karatu ta gidan rediyo da gidan talabijin a jihar Legas "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?