
Coronavirus: 'Yar Buhari ta killace kanta bayan dawowa daga London
Thursday, 19 March 2020
Comment
A wasu jerin sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter, Aisha Buhari ta ce a ranar Alhamis ne 'yar tata wacce ba ta fadi sunanta ba ta koma Najeriyar daga Birtaniya.
Ta ce yarinyar ta killace kan nata ne saboda shawarar da Ministan Lafiya na kasar suka bayar ba wai don ta nuna alamun cutar ba.
Kuma ta yi kira ga iyaye su dauki iirn wannan matakin idan yaransu sun dawo daga tafiya.
Kazalika uwargidan shugaban kasar ta ce ta rufe ofishinta na tsawon mako biyu saboda wasu ma'aikatan ofishin nata sun dawo daga Birtaniya.
Good afternoon Nigerians,— Aisha M. Buhari (@aishambuhari) March 19, 2020Earlier today my daughter returned from the UK being among the high Burden listed countries of COVID-19. pic.twitter.com/cku3bzcIJS
Aisha Buhari ta kuma yaba wa gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya bakwai da na jihar Neja da Kwara kan matakan da suka dauka na dakile yaduwar cutar.I commend the North Western Governors including Niger and Kwara on preventive measures taken to curb the spread of COVID-19 at their security meeting yesterday in Kaduna.— Aisha M. Buhari (@aishambuhari) March 19, 2020
Ta kara yin kira ga mutane da su ci gaba da bin shawarwarin jami'an lafiya don kauce wa yaduwar cutar.
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Coronavirus: 'Yar Buhari ta killace kanta bayan dawowa daga London"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?