
Coronavirus: Kamfanin BUA Group ya bayar da gudunmowar N1bn
Friday, 27 March 2020
Comment
Mai kamfanin na BUA Group, Abdul Samad Rabiu wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya kara da cewa baya ga kudin, kamfanin ya kuma bayar da kayan aiki da suka hada da injina da na'urorin gwaji da sauransu ga jihohi 9 na kasar.
Jihohin dai su ne Lagos da Kano da Adamawa da Edo da Kwara da Rivers da Abia da Akwa Ibom da kuma Sokoto.
Abdul Samad ya kuma ja hankalin sauran kamfanoni masu zaman kansu da su tallafa wa gwamnati wajen ganin an dakile wannan annoba, inda ya kara da cewa kamfanin nasa zai bayar da naira bilyan dayar ne ta hanyar babban bankin Najeriya.
BUA donates N1billion cash and also orders medical equipment to support COVID-19 response.https://t.co/b3VyA4ITO6#BUAGroup #UnlockingOpportunities #BUACares pic.twitter.com/NFIqxPJJKQ— BUA Group (@BUAgroup) March 26, 2020
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Coronavirus: Kamfanin BUA Group ya bayar da gudunmowar N1bn"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?