
Buhari ne ya bayar da umarnin tumbuke Sarkin Kano – Kwankwaso
Wednesday, 11 March 2020
Comment
Tsohon gwamnan jahar Kano, kuma wanda ya nada tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa tubuke rawanin Sarkin Kano umarni ne daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari. BBC ta ruwaito Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da ya yi da ita game da batun tsige tsohon Sarkin na Kano, inda ya bayyana hakan a matsayin abin bakin ciki ga jahar Kano, Najeriya da ma duniya gaba daya.
Game da zargin da ake masa tare da magoya bayansa yan Kwankwasiyya game da rura rikicin dake tsakanin Gwamna Ganduje da tsohon Sarkin Kano kuwa, Kwankwaso ya ce su a kullum suna bayan mai gaskiya ne. Sa’annan ya bayyana cewa babban abin da yasa sarkin ya gamu da fushin Gwamna Ganduje bai wuce bukatar da ya bayyana ba na cewa a baiwa duk wanda ya ci zaben gwamnan Kano nasararsa. A wani labari kuma, wani matashi mai ji da kardi daga jahar Jigawa ya kaddamar da tattaki zuwa jahar Kano domin taya sabon Sarkin Kano, mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero murnar darewar karagar mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan matashi mai suna Umar dan asalin jahar Kano ne, amma yana karatu a jami'ar gwamnatin tarayya dake birnin Dutse na jahar Jigawa. Murna da farin ciki da ya turnuke Umar biyo bayan sanar da Aminu Ado a matsayin sabon Sarkin Kano ne yasa ya fara wannan tattaki domin yin jinjinar ban girma, tare da bayyana ma sabon sarkin farin cikinsa da kuma fatan alheri. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Buhari ne ya bayar da umarnin tumbuke Sarkin Kano – Kwankwaso "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?