
Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya
Tuesday, 3 March 2020
Comment

Kashe-kashen musulmai a kasar Indiya sakamakon hargitsi tsakanin Musulmai da mabiya addinin Hindu a kan wata doka ya zamo sanadin rasa rayuka 27 a birnin New Delhi a ranar Laraba. A yayin da babban birnin kasar Indiyan ke fuskantar hari mafi muni a kan Musulmai a wannan lokacin, Firam minista Narendra Modi ya wallafa
wanda alhakin kwantar da tarzomar birnin Delhi din ta rataya a kan shi, ya kara ziyartar Jafrabad a yammacin Laraba don duba yanayin tsaron da kuma yin jawabi ga jama'ar. "Da izinin Allah zaman lafiya zai wanzu," ya ce a yayin da yake kewaye da tawagar jami'an tsaro. "An shawo kan komai kuma jama'a sun gamsu. Ina da tabbacin cewa hukumomin tsaro na yin abinda ya dace." Ya kara da cewa.
Jafrabad na daya daga cikin yankin da tarzomar ta fi tashi a birnin New Delhi. Kwanaki hudu kenan da ake ta tashin hankulan inda aka kashe mutane 27 tare da raunata mutane 200. A wannan yankin ne kuma aka samu wata budurwa da ta tsare Doval inda ta sanar da shi cewa ita daliba ce kuma basu iya bacci da dare. Rikicin bai ritsa da ita ba amma kuma bata iya karatu.
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Birnin Delhi ya zama mayankar al'ummar Musulmi a kasar Indiya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?