
Babu ruwana da lamarin tunbuke sarkin Kano - Buhari
Wednesday, 11 March 2020
Comment
Fadar shugaban kasa ta yi martani kan zarge-zargen da ake yi cewa da sanin shugaba Muhammadu Buhari aka tunbuke tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Zaku tuna cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya bada umurnin tsige sarki Sanusi.
Garba Shehu yace ” Babu ruwan shugaba Muhammadu Buhari da kwancewa Muhammadu Sanusi II rawanin sarautar Kano. Dukkan rade-radin da ake yi karya ne kuma siyasa ne kawai.”
”Ba sunnar Buhari bane sa baki cikin lamarin jihohi a kasar nan, sai dai idan lamarin na da illa ga kasa. Amma idan lamarin zai shafi tsaron kasa, ta ya zama wajibi kamar yadda doka ta tsara.”
”Kamar yadda take cikin kundin tsarin mulki, nadi da cire sarakunan gargajiya hakkin gwamnatocin jiha ne. Babu adalci yan adawar siyasa su rike hada gwamnatin tarayya da lamarin jihar Kano.”
A bangare guda, Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar, wanda shine shugaban wani kwamitin yin sulhun a tsakanin tsohon Sarki Muhammadu Sanusi da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, da samar da zaman lafiya a Najeriya, ya bayyana cewa sun yi iya kokarin bakinsu domin ganin sun kawo sasanci a tsakanin shugabannin biyu, amma abun ya ci tura.
A wata hira da ya yi da muryar Amurka, Abdulsalami, ya ce duk da yake sun zauna a lokuta mabanbanta da gwamnan jahar Kano da kuma tsohon sarki Sarki Sanusi na biyu, kafin suka yi wani zaman tare da su a lokaci daya, hakarsu bata cimma ruwa ba na neman a sasanta su, har abun ya kai ga tsige Sarkin, kasancewa gwamna ne mai wuka kuma mai nama.
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Babu ruwana da lamarin tunbuke sarkin Kano - Buhari"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?