
Babbar magana: Daya daga cikin makusantan mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya kamu da cutar Coronavirus
Saturday, 21 March 2020
Comment
kuma hakan ya zo ne a lokacin da ake cikin damuwa dangane da lafiyar 'yan siyasa na birnin Washington, manyan ma'aikatan gwamnati da kuma wadanda suke yi musu aiki.
Katie Miller, sakatariyar Mike Pence, ta ce: "Yau da yamman nan mun samu labarin cewa daya daga cikin ma'aikatan ofishin mataimakin shugaban kasa ya kamu da cutar Corona. Sai dai daga shugaban kasa Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence babu wanda ya hadu da wannan mutumi.
Yanzu dai ana bincike akan mutanen da ya hadu da su." Donald Trump ya zabi Pence domin ya jagoranci masu bincike akan Coronavirus na fadar shugaban kasar, wacce ake gabatar da rahoto a kullum. An tabbatar da babu cutar dai a jikin shugaba Donald Trump bayan gwajin da aka gabatar a jikinsa,
Bayan ya gana da daya daga cikin manya a kasar Brazil a birnin Florida. Da yawa daga cikin mutanen da suka hadu da dan kasar Brazil din wanda aka samu cutar a jikinsu an tabbatar da cewa suna gabatar da ayyukansu daga gida ne. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Babbar magana: Daya daga cikin makusantan mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya kamu da cutar Coronavirus "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?