
Babban magana: Za a gurfanar da gwamnan Taraba a gaban kotu
Monday, 2 March 2020
Comment
- Jam'iyyar APC reshen jahar Taraba ya sha alwashin gurfanar da gwamnan jahar, Ishaku Darius wanda ya kasance dan jam’iyyar PDP a gaban kotu idan har bai mika ragamar mulki ga mataimakinsa ba - Shugaban jam’iyyar APC a jahar, Ibrahim Elsudi ya bayyana cewa sun bai wa gwamna Darius wa’adin mako guda don ya mika mulkin ga mataimakinsa ko su hadu a kotu
A bangare guda, an yi kira ga yan majalisar sokokin jihar Taraba su yi gaggawa tsogi gwamnan jihar, Darius Ishaku, kan kauracewar da yayi jihar tun shekarar 2019. Watanni biyu cir rabon da gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya taka jiharsa ba kuma mutan jihar sunce yanayin gudanar da aikin gwamnatin jihar Taraba ya ja tsaya cik saboda rashin gwamnan, Rahoton Daily Trust. Aikin shi na karshe kafin barin jihar shine gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin jihar a ranar 19 ga watan Disamba 2019.
Jim kadan bayan gabatarwar, aka samu rahoton cewa ya bar Jalingo a ranar 22 ga watan Disamba 2019 kuma tun daga nan ba’a sake ganin kafarsa ba. Gwamnan bai bar wa mataimakinsa, Alhaji Haruna Manu, rikon kwarya ba, sannan bai sanarwa yan majalisar jihar ba. Bincike ya nuna cewa tun daga 19 ga watan disamba 2019 har yau, ba’a sake ganawar majalissar zantarwar jihar ba. Har ila yau, ba wani aiki da yake gudana yanzu a Jalingo, mutane da yawa na jihar sun nuna damuwar su game da rashin gwamnan. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
0 Response to "Babban magana: Za a gurfanar da gwamnan Taraba a gaban kotu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?