--
An tsaurara matakan tsaro a fadar Kano gabanin sanar da sabon sarki

An tsaurara matakan tsaro a fadar Kano gabanin sanar da sabon sarki

 Rundunar jami'an tsaro a ranar Litinin ta tsinkayi fadar Sarkin Kano da ke jihar Kano. Wannan ya biyo bayan tumbuke Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da ofishin gwamnan jihar yayi. Rundunar jami'an tsaron da suka hada da 'yan sanda da jami'an NSCDC ne suka mamaye harabar fadar, 

kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito. Gwamnati ta jibge jami'an tsaro a fadar ne gabanin sanar da sabon sarkin da zai maye gurbin sarki Sanusi, kamar yadda jawabin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana bayan sanar da tsige Sanusi. 

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnatin jihar Kano ta tsige mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu. Hadimin gwamnan Kanon kan sabbin kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 9 ga watan Maris, 2020.

Jami'an tsaro sun mamaye fadar sarkin Kano Source: Twitter 

Hakazalika, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya saki jawabi kan dalilin da yasa gwamnatin jihar ta tunbuke sarkin Kano daga kujerarsa. Ya ce an kwancewa Sanusi Lamido Sanusi rawani ne saboda yan zubar da mutunci da kuma ko oho da dokokin masarautar.

Baya ga haka, Usman Alhaji ya ce Sarkin ya daina halartan dukkan ganawa da gwamnatin jihar ta shirya ba tare da wani uzuri kwakkwara ba kuma hakan rashin biyayya ne ga gwamnati.

Yace: "Ya kamata a sani cewa a lokuta da dama, Malam Muhammadu Sanusi II ya kasance mai karya sashe na 3 na dokar masarautar kuma idan aka cigaba da zuba masa ido, zai lalata mutuncin masarautar." "An tunbukeshi ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar" LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "An tsaurara matakan tsaro a fadar Kano gabanin sanar da sabon sarki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?