--
An sanya doka mai tsauri akan maza masu yin auren jinsi a kasar Singapore

An sanya doka mai tsauri akan maza masu yin auren jinsi a kasar Singapore

- Wata babbar kotun kasar Singapore ta jaddada wata tsohuwar doka tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka

- Dokar dai ta haramta luwadi ne tsakanin maza amma bata dubi haramta madigo tsakanin mata ba - Lauyoyin biyu masu kare wasu maza uku ne suka sha mugun kaye a gaban kotun bayan da alkalin babbar kotun yayi watsi da karar Wata dokar kafin zuwan turawan mulkin mallaka wacce ta haramta luwadi an sake jaddada ta a wata babbar kotun Singapore a ranar Litinin 30 ga watan Maris.

Dokar wacce ba ta shafi 'yan madigo ba ta samu kalubale mai tarin yawa daga masu rajin kare hakkin dan Adam bayan kasar Indiya ta dage irin ta a 2018. Lauyoyi biyu da suka wakilci mutane uku: Johnson Ong Ming, Roy Tan Seng Lee da kuma Bryan Choong Chee Hong, sun kalubalanci dokar da ta haramta luwadi.

Amma kuma, mai shari'a See Kee Oon wanda ya jagoranci shari'ar, ya yi watsi da bukatar. Ya ce; "Babbar kotun tayi watsi da dukkan bukatu ukun. Akwai bukatar doka a yayin daidaita bukatar jama'a da matsayarsu." A yayin martani ga hukuncin, Bryan Choong ya ce bai ji dadin hukuncin ba. Ya kara da bayyana cewa hankalin shi har yanzu yana kan dage dokar. Wannan hukuncin ya biyo baya ne yayin da Firayim Minista Lee Hsein Loong ya bayyana cewa Singapore ba za ta iya kawar da kai a kan iren-iren lamurran nan ba.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "An sanya doka mai tsauri akan maza masu yin auren jinsi a kasar Singapore"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?