
An kama mai wallafa labaran karya kan coronavirus
Monday, 16 March 2020
Comment
'Yan sanda a Kenya sun kama wani mutum mai shekara 23 da ke wallafa labaran karya kan yaduwar coronavirus a kasar.
An kama Elijah Muthui Kitonyo ne a garin Mwingi da ke gabashin Kenya kan ikirarin da yake yi cewa gwamnati tana bayar da bayanan da ba sahihai na kan mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar a kasar.
Wani sakon Twitter da aka wallafa a shafin karya da aka yi ta yada wa a shafukan sada zumunta a karshen makon nan, ya yi ikirarin cewa mara lafiyar ya shiga kasar ne daga birnin Rome na Italiya, ba ta Amurka daga Landan ba kamar yadda gwamnatin ta fada.
Hukumar bincike kan masu aikata miyagun laifuka ta kasar ce ta tabbatar da batun kamun nasa a shafin Twitter.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YElijah Muthui Kitonyo aged 23 years has been arrested in Mwingi for publishing misleading and alarming information on Corona virus.— DCI KENYA (@DCI_Kenya) March 15, 2020
He will be charged for publishing false information that is calculated or results in panic contrary to section 23 of the Computer Misuse...
/1 pic.twitter.com/qH9PBVoS8n
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "An kama mai wallafa labaran karya kan coronavirus"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?