
Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero sun ziyarci Sanusi Ado Bayero
Tuesday, 24 March 2020
Comment
Mun samu labari cewa Sarakunan kasar Bichi da Kano watau Nasiru Ado Bayero da Aminu Ado Bayero sun hadu da Alhaji Sanusi Ado Bayero. Sababbin Sarakunan sun hadu da ‘Danuwansu ne yayin da su ka kai masa ziyara a gidansa. Sarakunan sun kai ziyarar ne a farkon makon nan.
Wannan labari ya zo gare mu ne ta wani bidiyo da aka wallafa a shafin Masarautar Kano da ke dandalin sadarwa na zamani na Tuwita a jiya. Shafin @HrhBayero su kan dauko labaran da su ka shafi Masarautar Kano ta Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero tun bayan da yau kan gadon mulki.
A bidiyon an bayyana cewa Sarakunan sun tashi da kafafunsu ne sun kai wa babban Yayan na su ziyara a gidansa da ke cikin Birnin Kano a jihar.
Bisa dukkan alamu an dauki lokaci tsohon Ciroman ba ya kasar Kano. Legit.ng Hausa ta na tunanin wannan ne karon farko da Sarakan su ka hadu. Idan ba ku manta ba tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne ya tubewa Sanusi Lamido Ado Bayero rawanin Ciroman Kano bayan ya hau mulki. Sarki Muhammadu Sanusi II ya zargi Takwaransa Sanusi Ado Bayero da kin yi masa mubaya’a bayan dukkansu sun nemi kujerar Sarkin Kano a 2014.Mai martaba sarkin Kano da me martaba sarkin Bichi sun kaiwa dan uwansu kuma wansu mai girma Ciroman Kano murabus ziyara gidansa dake Kano. Alhamdulillah Alhamdulillah— Masarautar KANO (@HrhBayero) March 23, 2020
Allah ya kara hada kanku pic.twitter.com/PIe5cNXwR7
A dalilin haka ne Ciroma Nasiru Ado Bayero ya samu sarautar Bichi. Yanzu dukkansu sun zo sun gaida Yayan na su, sai dai ba a ji abin da su ka tattauna ba.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YInji hasken fadar Kano. pic.twitter.com/4e9tnxdSwU— Masarautar KANO (@HrhBayero) March 14, 2020
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero sun ziyarci Sanusi Ado Bayero "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?