
Abin da nafi so nayi kafin na mutu shine na kwanta akan katifa - Tsohuwa
Thursday, 12 March 2020
Comment
- A cewar Yara wacce take talaka ce kuma ba ta gani, ta ce bata samu irin rayuwar da take so ba, saboda akwai raneku da yawa da ko abinci ba ta iya samu ta ci saboda babu
- Yara ta bayyana cewa tana da yara biyu amma dukkansu sun koma kudancin Ghana da zama
Wata tsohuwa wacce ba ta gani mai suna Yara Kwanjit dake Saanbona a yankin arewa maso gabashin kasar Ghana ta bayyana babban burinta a rayuwa, inda ta bayyana cewa abinda tafi so a yanzu shine ta kwanta akan katifa.
A yadda Yara ta bayyana, 'ya'yanta guda biyun duka sun gudu yankin kudancin kasar Ghana domin su cigaba da zama a can, kuma duka a cikin 'ya'yan nata guda biyu daya ne kawai yake kawo mata ziyara.
Ta ce ta san duk da cewa ba ta san yawan shekarunta ba, amma ta san bai kamata ace tayi irin tsufan da tayi yanzu ba, ta san cewa tsufanta yana da nasaba da rashin kudi.
A yadda take Yara ta bayyana cewa akwai raneku da yawa da suke zuwa su wuce ba tare da taci abinci ba, ta ce zama talaka yana nufin rashin samun abinda mutum yake so a rayuwa.
Yara ta ce abinda tafi so a rayuwarta yanzu kafin ta mutu shine ta kwanta akan katifa.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "Abin da nafi so nayi kafin na mutu shine na kwanta akan katifa - Tsohuwa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?