A karshe; Shugaba Buhari na wasa ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan coronavirus
Sunday, 22 March 2020
Comment
Obinna Simon, wani dan Najeriya mai wasan barkwanci da ke matukar kama da shugaban kasa, Muhammadu, ya saki wani jawabi ga 'yan kasa inda a cikinsa ya yi magana a kan bullar annobar kwayar cutar coronavirus. Fitaccen mai wasan barkwancin, wanda aka fi sani da 'MC Tagwaye',
ya saki jawabin ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da guna-guni a kan jinkirin da shugaba Buhari ke yi wajen gabatar da jawabi ga 'yan kasa a kan annobar coronavirus. Kamar yadda ya saba yin magana cikin kwaikwayon muryar Buhari, MC Tagwaye ya bukaci 'yan Najeriya su mayar da hankali wajen biyayya ga hanyoyin dakile yaduwar COVID-19. A cikin sakon faifan bidiyon mai tsawon dakika 140 da ya wallafa a shafinsa na 'Tuwita'
(@MC_Tagwaye), ya ce, "shugaba Buhari ya hana dukkan jami'an gwamnati fita kasashen waje tare da daukan matakan dakile yaduwar kwayar cutar corona a fadin kasa.
MC Tagwaye Source: Twitter "Dukkan kasashen duniya sun dauki matakan ganin cewa kwayar cutar ba ta cigaba da yaduwa a kasashensu ba. An dauki mataki a kan cutar ne ba don a takurawa jama'a ba, sai don a karesu daga kamuwa da ita. "Najeriya, kamar sauran kasashen duniya, ta dauki matakai daban-daban domin dakile kwayar cutar corona. Matakan sun hada da;
"Haramtawa jami'an gwamnati fita kasashen ketare da kuma hana jirage daga wasu kasashen duniya sauka a Najeriya. Bayan an dauki wasu sauran matakai a cikin gida domin hana kwayar cutar uaduwa." Kalli faifan bidiyon:
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YThe National Broadcast you all have been waiting for😊— Mc Tagwaye (@mc_tagwaye) March 19, 2020
Can I rest now 🤔 pic.twitter.com/YdfHAXT3OV
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
0 Response to "A karshe; Shugaba Buhari na wasa ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan coronavirus "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?