
FGN & MTN NG:/ RIKICIN MTN DA GWAMNATIN TARAYYA
Monday, 13 January 2020
Comment
A Karshe Ministan Shari'a, Malami Ya Mika Rikicin Ga Hukumar FIRS Da Kwastam
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a SAN, Abubakar Malami a karshe ya dakata daga ci gaba da warware takaddamar dake tsakanin MTN da Gwamnatin Tarayya zuwa Hukumar Kula da Haraji ta Tarayyar Nijeriya da kwastan.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Dakta Umar Jibrilu-Gwandu, Mataimaki na Musamman kan Kafafen yada labarai a Ofishin Babban Sakatare ga Ministan Shari’a ya bayar ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a, 10 ga Janairu, 2020.
Sanarwar ta ce, Ministan ya sanar da sakon a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 8 ga Janairu, 2020 da aka yi wa Lauyan MTN; Messrs Wole Olanipekun & Co.
0 Response to "FGN & MTN NG:/ RIKICIN MTN DA GWAMNATIN TARAYYA"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?