
AL'AJABI: Budurwa Ta Bankawa Kanta Wuta A Garin Gusau Saboda Saurayinta Ba Shi Da Kudin Aurenta
Monday, 9 September 2019
Comment
Wata yarinya mai suna Aisha dake anguwar Albarkarwa dake nan garin Gusau jihar Zamfara ta yaiyafawa kanta fetur ta kestawa kanta ashana.
A zantawarmu da mai unguwar anguwar Alh Aminu Muhammad ya shaida mana cewar lokacin da abun ya faru yarinyar ta fito waje tana kururuwa na neman agaji a waje yayin da su matasa suka yi kanta tare da kashe mata wutar da tu ni ta ci zarafinta.
Yanzun haka dai wannan boyar Allah tana nan kwance rai kwa-kwai mutu kwa-kwai a gidansu sanadiyar rashin kudin zuwa asibiti.
Kamar yadda Mai Unguwar shiyar ya shaidawa manema labaru ko da abun ya faru naira 750 kacal ne a gidan don haka ba zarafin zuwa asibiti da wannan ake neman masu tausayi kuma masu hali za su ceto rayuwar Malama Aisha.
Dafatar Allah yakaremu da aikata aikin dana sani.
0 Response to "AL'AJABI: Budurwa Ta Bankawa Kanta Wuta A Garin Gusau Saboda Saurayinta Ba Shi Da Kudin Aurenta"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?